Manyan labarai daga cikin wasu jaridun Turkiyya 12.10.2017

Manyan labarai daga cikin wasu jaridun Turkiyya 12.10.2017

Manyan labarai daga cikin wasu jaridun Turkiyya 12.10.2017

Babban jaridar Yeni Şafak na cewa tawaga daga Amurka zasu shigo Turkiyya sati mai zuwa don warware matsalan dakatar da bayar da Viza a stakanin kasashen biyu. Mataimakin sakatare nam usanman a ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya bayyana hakan. A lahadin data gabata ne ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana dakatar da bayar da Visa ga Turkawa, a yayinda ita Turkiyya ta dauki matakan hakan a kasarta.

Babban jaridar Star na cewa ministan ma’adanai da makamashin Turkiyya Berat Albayrak ya bayyana cewa Turkiyya zata gina wani katabaren bututun man fetur da gas a yankin Mediterranean. Ministan ya kara da cewa wannan zai bunkasa lamurkan makamashin kasar tare da habbaka tattalin arziki.

Babban jaridar Sabah na cewa ma’aikatar tsaron Turkiyya ta bayyana gudanar da atasaye a wasu yankunan Iraq da Siriya domin samar da tsaro ta hanyar kauda ‘yan ta’addan yankunan. Za’a dai gudanar da atsayen ne a yankuna hudu da suka hada da yankin Hatay-Reyhananli, Idlib, Idlib- Dar da kuma Afrin. Babban makasudin yin hanka shine kauda ‘yan ta’addar PYD, PKK da DEASH.

Babban jaridar Vatan na cewa Turkiyya da Iran zasu hada karfi da karfe don magance dukkan nau’okan ta’addanci da suka hada da PKK da DAESH a yankunansu. Zasu yi haka taa kafa tsaro a iyakokinsu tare da hadin gwiwar sojojin kasashen biyu.

Babban jaridar Haber Türk na cewa babban sakataren ma’aikatar tsaron Turkiyya Ismail Demir ya bayyana cewa za’a fara kera wasu nau’okan tankokin yaki a kasar Turkiyya. Haka kuma tsohon ministan tsaron Turkiyya Fikri Işik a watan Yuli ya bayyana cewa kasar Turkiyya ta soma shirye-shiryen kera na’urorin tsaro masu guba a kasar. Za’a fara wadannan muhimman kere keren ne don inganta tsaro a cikin gida da waje.

 

 Labarai masu alaka