• Bidiyo

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Star na cewa, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya ziyarci kasar Sabiya inda ya halarcin taron 'yan kasuwar Turkiyya-Sabiya, kuma ya yi bayani game da hasashen habakar tattalin arzikin Turkiyya da kaso 5.1 maimakon kaso 2.5 da Asusun Bayar da Lamuni na Duniya ya yi. Erdoğan ya ce, yadda suka so tattalin arzikinsu ya habaka haka ya yi. Wannan wani labari ne na tsawon shekaru 15. Ya kara da cewa, Turkiyya ta sake nuna wa duniya cewa, ta magance matsalar yunkurin juyin mulkin da akaso yi mata.

Babban labarin jaridar Haberturk na cewa, Shugaban kasar Sabiya Alexander Vuçiç ne ya gayyaci shugaban kasar Turkiyya Recep tayyip Erdoğan zuwa kasarsa inda kuma ya halarci wata liyafar cin abincin dare da aka shirya masa. A yayin cin abincin ministan harkokin wajen Sabiya Ivitsa Daviç ya yi abin mamaki na rera wakokin Turkiyya. Shugaba Erdoğan, matarsa Aminda, Shugaban Rundunar Sojin Turkiyya Hulusi Akar na daga cikin manyan mutane da suka halarci zaman cin abincin. 

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, Injiniyoyin Turkiyya sun sake yin nasara inda suka samar da wata na'urar tabbatar da ingancin gwal. Inginiyoyin sun samar da na'urar ne karkashin tallafin Hukumar Bayar da Tallafin Kimiyya da fasahar kere-Kere ta Turkiyya TUBITAK. A watan Janairun 2018 ne za a fara amfani da na'urar a Dubai da wasu kasashen Larabawa.

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, dan wasan Turkiyya Cenk Tosun da ya jefa kwallo a raga a wasan da Tukiyya ta yi da Finlan wanda aka tashi biyu da biyu zai ci gaba da kasancewa a kungiyarsa. Jaridar the Sun ta Ingila ta rubuta cewa, Kungiyar Crystal Palace na son sake tattauna wa da Cenk. Mai horar da 'yan wasan Crystal Roy Hodgson ya ce, yana son ganin dan wasan na Beşiktaş a kungiyarsu a watan janairu. Labarai masu alaka