Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yi sabon jawabi game da kuri'ar raba gardama da aka jefa a yankin Kurdawan Arewacin Iraki a ranar 25 ga watan Satumba inda ya ce,  duk mutanen da suka bayar da dama aka gudanar da waccan kuri'ar raba gardamar to su tabbatar za su dandana kudarsu. Ba su gano me suka yi ba. Barzani sai ya hakura da wadannan mutane.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, a garin Mugla da aka kama wasu 'yan ta'addar PKK 7 an sake kashe wasu 5 a wannan karon. Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Turkiyya ta ce, 'yan ta'addar na baro Lazkiye tare da kokarin zuwa yankin tekun Aegean. Ministan harkokin Waje Sulayman Soylu ya ce,  a yanzu 'yan ta'addar na neman sabbin hanyoyin shiga wasu yankunan daban bayan da suka samu damar bulla a Afrin daga Iran.

Babban labarin jaridar Star na cewa, Ministar Harkokin Iyali da Jindadinsu ta Turkiyya Fatma Betul Sayan kaya ta gana da wakilan mata na kungiyoyin fararen hula domin taimaka wa al'umar Arakan. Ministar ta yi kira ga kasashen duniya da cewa, me ya sa kasashe suka tsaya suna kallon yadda ake zaluntar mata da yara kanana ba tare da cewa komai ba, to ko da kowa zai zama makaho, kurma, bebe da gurgu to Turkiyya ba za ta zama ba kuma za ta taimaka wa Musulman Arakan da ake zalunta.

Babban labarin jaridar Haberturk na cewa. a yammacin wannan rana Turkiyya za ta kara da kasar Aislan a wasannin neman cancantar zuwa gasar cinn kofin duniya da za a yi a Rasha a shekarar 2018 mai zuwa. Turkiyya na neman nasara a wasan wanda dan kasar Polan Szymon Marciniak zai yi alkalanci.Labarai masu alaka