Taƙaitatun labarai daga wasu manyan jaridun Turkiyya 05:10:2017

Taƙaitatun labarai daga wasu manyan jaridun Turkiyya 05:10:2017

Taƙaitatun labarai daga wasu manyan jaridun Turkiyya 05:10:2017

Babban jaridar Vatan na cewa ɗaya da ga cikin kanfunan dake saye da sayarwa ta yanar gizo a Turkiyya mai suna Hepsiburada.com ya rataɓa hannu aiki bay ɗaya da babban kamfanin Goldman Sachs Group. Hakan dai zai habbaka lamurkan kasuwanci ƙasar tare da bunƙasa lamurkan saka hannun jari. Akan wannan yunkuri ne shugaba Erdoğan ya gana da wanda ya kirkiri kanfanin Alibaba.com Jack Ma bayan taron ƙolin Majalisar Dinkin Duniya a Amurka.

Babban jaridar Yeni Şafak na cewa shahararren ɗan wasan kwaikwayon Bollywood Aamir Khan ya ziyarci Turkiyya a dalilin gayyatar da ma'aikatan harkokin al'adu ta yi masa. Ya shaidawa manema labarai a filin jirgin sama Istanbul da cewa ya jima ya na sun ya ziyarci kasar domin fina finan ƙasar suna burge shi. Daga bisani yayi godiya ga irin gagarumin tarbon da aka yi masa.

Babban jaridar Sabah na cewa Turkiyya zata fara ƙaddamar da wata tsarin kasuwanci a duniya, Inda zata ɗauki ƴan kabilar Turkawa da ke zaune a ƙasashe daban daban a matsayin jakadoji kasuwanci, hakan zai bunƙasa saye da sayarwa kayayyakin ƙasar a fadin duniya.

Sai babban jaridar Star da ke cewa Turkiyya ta nemi a saka gadar Erdirne da ke ƙasar ta a matsayin gadar dutse mafi tsawo a cikin kundin tarihin Guinness world records. An dai yi gadan ne a tsakanin shekarar 1426-1443 a lokacin Sultan Murat na biyu da duwatsu na musamman. Gadan nada tsayin mita dubu da ɗari uku da talatin da uku da kuma faɗin mita shida da ɗigo tamanin.

Sai kuma babban jaridar Haber Türk data rawaito cewa an bayyana ɗan wasan ƙwallon ƙafan Turkiyya Berke Özer ɗan shekaru 17, mai tsaron gida a matsayin ɗaya da ga cikin kwararrun ƴan wasan ƙwallon kafa 60 a duniya.

 Labarai masu alaka