Turkiyya ta aike da sammace ga jakadan Amurka da ke Ankara

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta gayyaci jakadan Amurka a Ankara John Bass tare da bayyana masa cewa, ba za a amince da hukuncin da Amurka ta fitar ba na a kama jami'an staron shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan.

Rubutacciyar sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce, a ranar 16 ga watan Mayu a gaban gininofishin jakadancin Turkiyya da ke Washington an samu matsala inda sakamakon haka Amurka ta fitar da hukuncin kama jami'an tsaron shugaba Erdoğan, kuma Turkiyya ta shaida wa jakadan na Amurka ba ta lamunci wannan hukunci.

Babban Sakare a Ma'aikatar ne ya mika wa jakada Bass wannan bayani a rubuce.

Sanarwar ta kara da cewa, wannan mataki da Amurka ta dauka babban kuskure ne kuma ba ya kusa da doka kohakki. Kuma an samu matsalar da ta faru ne a Washington saboda kin daukar matakan da suka kamata da jami'an tsaron Amurka suka yi ne. Da a ce Amurka ta dauki matakan tsaro da suke ba wa shugabannin idan sun ziyarci kasar to da hakan ba ta faru ba.

Turkiyya ta ce, wannan hukunci babu adalci da tunani a cikinsa, a saboda haka ba za a amince da shi ba sam.Labarai masu alaka