Turkawa sun hada kai domin murkushe yunkurin juyin mulki

Daruruwan dubban Mutane daga sassa daban-daban na kasar Turkiyya sun hada karfi da karfe domin murkushe yunkurin juyin mulkin da wasu sojoji suka yi a kasar.

Turkawa sun hada kai domin murkushe yunkurin juyin mulki

Daruruwan dubban Mutane daga sassa daban-daban na kasar Turkiyya sun hada karfi da karfe domin murkushe yunkurin juyin mulkin da wasu  sojoji suka yi a kasar.

An rawaito cewa a safiyar Asabar din nan wadanda suka yi yunkurin juyin mulki sun arce tare da barin makamai da tankokin yaki a kan gadar Basfaras.

Wani jami'in kasar Turkiyya ya yi bayani a kafar yada labarai ta Anadolu Agency cewa akalla mutane 60 wadanda suka hada da jami'an tsaron kasa 17 da farar hula 2 sun rasa ransu.

A yayin da yake magana a gidan talabijin na CNN Turk,firaministan kasar Turkiyya Binali Yildrim ya sanarwa al'uma cewa an kashe daya daga cikin manya-manyan hafsosin sojin kasar Turkiyya wanda ya kasance a sahun gaba a wajen shirya juyin mulkin.

Wasu majiyoyin sun tabbatar da cewa an kama akalla mutane 130 wadanda ake zargin suna da hannu a wannan aika-aikan.

A sanyin safiyar yau,shugaba Erdoğan ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Istanbul,inda ya jinjina wa dubban mutanen da suka tarbe shi.

An tabbatar da cewa malamin nan mai sun Fethullah Gulen wanda ya yi hijira zuwa kasar Amurka ne ya yi ruwa da tsaki a wajen shirya wannan juyin mulkin.

TRTWorldLabarai masu alaka