Ambaliyar ruwa ta kashe shanu sama da dubu dari uku a Ostireliya

Shanu sama da dubu 300,000 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a garin Townsville na jihar Queensland dake kasar Ostireliya.

Ambaliyar ruwa ta kashe shanu sama da dubu dari uku a Ostireliya

Shanu sama da dubu 300,000 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a garin Townsville na jihar Queensland dake kasar Ostireliya.

Labaran ta Sky News dake Ostireliya ya fitar na cewa, sakamakon ruwan sama kamar da bakn kwarya da aka samu a makon jiya a garin Townsville da kewaye an tafka asarar dukiyoyi da yawa.

An bayyana cewar yanki da ya ya sha fama da matsalar fari, a yanzu kuma ambaliyar ruwa ta janyp asarar kusan dala miliyan 300 inda shahu sama da dubu 300,000 suka halaka.

A lokacinda dubunnan gidaje suke ci gaba da kasancewa a karkashin ruwa, ruwan da ya balle daga madatsun ruwa na shiga gonaki tare da halaka dukkan dabbobi, wasu kuma saboda rasa abinda za su ci ya sanya suka mutu.

Shugaban gundumar Richmond, John Wharton ya fadi cewa, kowanne daya daga cikin shanun da suka mutu ya kai darajar dala dubu daya.

Ya ce, wannan adadi na gona daya ne kawai, idan aka je sauran gundumomi za a samu an yi asarar shanu kusan miliyan 7 zuwa 8.

Tuni aka fara aikewa da abincin dabbobi da jirage masu saukar ungulu domin a samu damar hana su mutuwa.Labarai masu alaka