Mahakar ma'adanai ta rufta da leburori a Afirka ta Kudu

Mutane 5 ne suka mutu sakamakon ruftawar mahakar ma'adanai a arewacin Afirka ta Kudu.

Mahakar ma'adanai ta rufta da leburori a Afirka ta Kudu

Mutane 5 ne suka mutu sakamakon ruftawar mahakar ma'adanai a arewacin Afirka ta Kudu.

Wani daga cikin mahukuntan yankin Speedy Mashilo ya fadi cewa, a yankin Gloria hatsarin fashewar wasu abubuwa ya afku a mahakar ma'adanan wanda hakan ya janyo rufatawar ta.

Bayan afkuwar lamarin ma'aikatan ceto sun bazama inda suka ciro jikkunan mutane 5 kuma ana tunanin akwai sauran ma'aikata 22 a karkashin kasar.

Mashilo ya ce, har yanzu ana ci gaba da aikin kokarin kubutar da mutanen.Labarai masu alaka