An fara bincikar tsohon Shugaban Kasar Maldives bisa zargin almundahana da dukiyar kasa

'Yan sanda da masu gabatar da kara a Maldives sun fara bincikar tsihon Shugaban Kasar Abdulla Yameen Abdul Gayoomm bisa zarginsa da aiyukan cin hanci da almundahana.

Sanarwar da Rundunar 'Yan sandan Kasar ta fitar ta ce, masu bincike sun samu bayanam dake tabbatar da Abdul Gayoomm ya yi ta'ammali da kudaden haram kuma tsohuwar minista Azime Shakur ta taimaka masa.

'Yan sandan sun kuma bukaci masu gabatar da kara da su tuhumi Gayoomm da Shakur da laifin bayar da bayanan karya.

 A watan Disamba ne aka fara bincikar Gayoomm bayan an gano ya yi amfani da asusun bankinsa wajen ta'ammali da kudaden haram.

An sanar da cewar Gayoomm ya yi nasarar zaben da aka yi a ranar 23 ga watan Satumba amma daga baya Hukumar Zabe ta sanar da dan takarar jam'iyyun gamayya Ibrahim Muhammad Salih a matsayin wanda ya yi nasara.

Salih ya sanar da zai bincike gwamnatin Gayoomm da shi kansa bisa zargin sun aikata cin hanci da rashawa a lokacin da ludayinsu ke kan dawo.Labarai masu alaka