Yajin aikin ma'aikata a Jamus ya janyo soke tashin jiragen sama 72

Sakamakon yajin aikin gargadi da ma'aikatan filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Hamburg dake Jamus suka yi don neman kara musu albashi an soke tashin jirage 72.

Sanarwar da aka fitar daga filin tashi da saukar jiragen saman ta ce, kungiyoyin kwadago na Verdi da Kombi ne suka yi kira da a yi yajin aikin na gargadi.

Sanarwar ta ce, sakamakon hakan an soke tashin jiragen sama 72 wanda yakan ya janyowa fasinjoji sama dadubu 9 matsala.

Ma'aikatan na neman a kara musu albashi da Yuro 275 amma masu ba su aikin sun ce wannan adadi da suke so ya yi yawa.Labarai masu alaka