Turkish Airlines ya yi jigilar fasinjoji miliyan 75.2 a 2018

Kamfanin Jiragen Saman Turkiyya Turkish Airlines ya samu karin kaso 10 cikin 100 na fasinjojin da ya yi jigila a shekarar 2018 sama da shekarar da ta gabace ta.

A shekarar 2018 kamfanin ya yi jigilar matfiya miliyan 75.2

An samu kari da kaso biyu wajen cikar jiragen saman kamfanin da ya kai kaso 82. Fasinjojin kasashen waje ya karu da maki3 wanda ya kama kaso 81 sai na cikin gida da karu da maki 1 da ya kama kaso 85.

Fasinjojin kasashen waje idan aka cire maso bi ta Turkiyya don zuwa wasu kasashen daban ya karu da kaso 12. A bangaren dakon kaya kuma an samu kari da kaso 25 cikin idan aka kwatanta da shekarar 2017 inda a 2018 ya kama tan miliyan 1.4.Labarai masu alaka