Shugaban Kamfanin Amazon zai rabu da matarsa

Shugaban Kamfanin Kasuwanci na Yanar Gizo Amazon Jeff Bezos da matarsa MacKenzie sun shirya za su raba aurensu da ya daukitsawon shekaru 25.

Shugaban Kamfanin Amazon zai rabu da matarsa

Shugaban Kamfanin Kasuwanci na Yanar Gizo Amazon Jeff Bezos da matarsa MacKenzie sun shirya za su raba aurensu da ya daukitsawon shekaru 25.

Shugaban na Kamfanin Amazon dake Amurka Jeff Bezos da matarsa MacKenzie sun dauki matakin kawo karshen alakarsu ta aure bayan shekaru 25 suna tare.

Bezos mai shekaru 54 da mujallar Forbes ta bayyana a matsayin wanda ya fi kowa kudi a duniya, shi da matar tasa mai shekaru 48 sun fitar da sanarwa ta shafin Twitter a lokacin guda cewar za su raba aurensu.

Sanarwar ta ce “Bayan daukar tsawon lokaci a matsayin mata da miji mun amince mu raba auren amma za mu ci gaba da abokantaka a tsakaninmu. Mun gamsu da yadda muka samu kanmu kuma mun yi rayuwar aure mai kau. Da mun san cewa za mu rabu bayan shekaru 25 da mun sake aure tare.”

Ma’auranat sun yi aure a shekarar 19993 kuma suna da ‘ya’ya 4.

A rahoton da mujallar Forbes ta fitar a watan Oktoba ne mujallar Forbes ta ce, Bezos ya mallaki tsabar kudi har dala biliyan 160.

 Labarai masu alaka