Kaso 38.5 cikin darin matasan Girka basu da aikin yi

Koda yake rashin aikin yi ya ragu a cikin watan Oktobar a shekarar 2018 a kasar Girka alkaluman da sunka kai 18.6 basu canza idan aka kwtanta dana watan daya gabata.

Kaso 38.5 cikin darin matasan Girka basu da aikin yi

Koda yake rashin aikin yi ya ragu a cikin watan Oktobar a shekarar 2018 a kasar Girka alkaluman da sunka kai 18.6 basu canza idan aka kwtanta dana watan daya gabata.

Hukumar kididdiga ta kasar Girka (ELSTAT), ta fitar da alkaluman rashin aikin yi a watan Oktoba. Alkaluman sun nuna cewa rashin aikin yi a kasar yakai lamba 18.6 cikin dari.

Yawan wadanda basu da aiki a kasar kuwa sunkai kaso 12 cikin dari a yayinda yawansu ya sauka da dubu 876.

A kasar ‘yan shekaru tsakanin 15-24 ne sunka fi fama da rashin aikin yi wadanda daga cikinsu ne anka fi samun raguwar rashin aikin. Daga cikin matasa dai an bayyana cewar vkaso 38.5 cikin dari ne basu da aiki.

Hukumar kasar na yunkurin rage alkaluman rashin aikin daga kaso 18.4 cikin dari a wannan shekarar zuwa kaso 18.2 a shekarar badi. Raguwar rashin aikin yi da anka samu sakamakon aikin half time ne da matasan ke yi.

Duk da dai kasar ta fattataki rashin aikin yi inda alkaluman rashin aikin sunka sauka daga kaso 28 cikin dari a shekarar 2013 zuwa 18, har ila yau it ace kasar da tafi ko wacce rashin aikin yi a cin yankin Turai.

A shekarar 2017 alkaluman rashin aiki a Girka ya kai kaso 21 cikin dari.

 Labarai masu alaka