Miliyoyin ma’aikata sun tsunduma yajin aiki a Indiya

Sakatare Janar na Kungiyar Kwadago ta Indiya Amarjeet Kaur ya bayyana cewa, kusan ma’aikata miliyan 200 sun tsunduma yakin aiki kwanaki 2.

Miliyoyin ma’aikata sun tsunduma yajin aiki a Indiya

Sakatare Janar na Kungiyar Kwadago ta Indiya Amarjeet Kaur ya bayyana cewa, kusan ma’aikata miliyan 200 sun tsunduma yakin aiki kwanaki 2.

Kaur ya ce, an fara yajin aikin a fadin kasar don nuna rashin amincewa ba manufofin gwamnati.

Kungiyoyin kwadagon sun soki yadda kayan masarufi suke tashi a Indiya inda suke neman da a kara yawan mafi karancin albashi tare da kyautata inshora da sauran hakkokin ma’aikata.

Ana samun nakasu a harkokin yau da kullum sakamakon yajin aikin inda aka bayar da hutun makarantu.

An bayyana cewar ‘yan sanda sun far wa wasu mutane da suka jefa musu duwatsu a jihar Bengal ta Yamma.Labarai masu alaka