Takunkumin Tattalin Arziki na 2 Ga Iran da Matsayin Turkiyya

A wannan makon ma mun sake kasancewa da Sharhin Dakta Cemil Dogac Ipek malami a sashen nazarin kasa da kasa dake jami’ar Karatekin a nan Turkiyya.

Takunkumin Tattalin Arziki na 2 Ga Iran da Matsayin Turkiyya

Takunkumin tattalin arziki da Amurka ta sakawa Iran a ‘yan kwanakin da suka gabata zai shafi dukkan kasashen duniya dake huldar kasuwanci da Iran din. A shirinmu na wannan makon za mu duba wannan takunkumi da aka saka wa Iran da irin tasirinsa ga manufofin Turkiyya a kasashen waje.A ranar 5 ga watan Nuwamba ne kashii na biyu na takunkumin tattalin arziki da Amurka ta saka wa Iran ya fara aiki. A karkashin takunkumin na biyu an hana Iran aksuwancin Man fetur, iskar gas, safarar jiragen ruwa, Inshora da bankin kasa da kasa. Tun wannan lpkacin aka takaita aiyukan kamfanin sarrafa man fetur na Iran da kamfanin tankokin kasar wajen mu’amala da kasashen waje. Hakan ya sanya aka fara saka takunkumin da ya fara aiki kan fitar da albarkatun man fetur zuwa waje. Alkaluman hukumar Facts Global Energy na cewa, tun watan Afrilu fitar da man fetur da Iran ke yi ya yi kasa sosai. Kuma bayan fara aiki da takunkumin gangar danyen mai da Iran ke fitarwa kullum na ganga miliyan 3 ya dawo kusan ganga miliyan 1. Ana hasashen cewar haka abin zai ci gaba har nan da tsakiyar shekarar dubu biyu da sha tara mai zuwa.

Kasashen dake fitar da albarkatun man fetur, sun bayyana cewar za su kra yawan man da suke fitarwa saboda wannan takuunkumi da aka kakabawa Iran. Wannan yanayi zai magance gibin da za a samu saboda haan Iran fitar da albarkatun man zuwa kasuwannin duniya. Bayan farashin mai ya dan tashi zuwa wani lokaci, amma daga baya zai daidaita ya koma yadda yake a yanzu. Saboda haka nan da wani dan lokaci farashin man zai tashi zuwa tsakanin dala 75 da 85 kowacce ganga wanda hakan ba zai bayar da mamaki ba. Alkaluman dake hannu na nuna ana da bukatar man fetur sosai. Rahoton Hukumar Kula da Makamashi ta Duniya na wata-wata  na cewa, yawan man da Kungiyar OPEC ke fitarwa ya karu da ganga dubu 100 wamda ya kama ganga miliyan 32 da dubu 780 a kowacce rana, wanda wannan ne mafi yawa a shekara dayan da ta gabata. A tsakanin mambobin kungiyar kuma a watan Satumba Saudiyya a kan gaba wajen fitar da albarkatun man fetur. Kasar ta dinga fitar da ganga miliyan 10 da dubu 520 a kowacce rana inda ta yi kari da ganga dubu 100.

Wannan takunkumi da Amurka ta kakaba na da wani batu mai muhimmanci. Wannan takunmi ba wai iya Iran ya tsaya ba, har da ma kasashen da suke mu’amala da ita. Amma an cire wasu kasashe da suke mu’amala da Iran daga takunkumin wanda har da Turkiyya a ciki. A gefe guda kuma wannan shine mataki mafi muni da gwamnatin Trump ta dauka kan Iran ta fuskar tattalina rziki.

Idan za a iya tunawa, A lokacin da trump yake takarar shugaban kasa ya nuna bai amince da yarjejeniyar Nukiliya da aka kulla da Iran a 2015 ba. Ya kuma yi alkawarin cewar idan aka zabe shi zai cire Amurka daga wannan yarjejeniya wadda cin amana ce. Haka kuwa aka yi a watan Mayun da ya gabata ya cika alkawarin da ya yi tare da cire Amurka ita kadai daga wannan yarjejeniya.

Madıgarar gwamnatin Trump kan cire wannan yarjejeniya ita ce, ba za ta hana Iran sarrafa Nukiliya ba. Sannan dalili na biyu na saka wa Iran takunkumi shi ne a tsayar da manufofinta munana da take yadawa a kasashen waje, tsoma bakinta a Siriya da kuma taimakawa Hizbullah da sauran kungiyoyin ta’adda.

 Trump na da manufar raba iran da wadannan yunkure-yunkıure nata ta hanyar kakaba mata takunkumai. Kamar yadda aka gani wannan shi ne shirin: wannan takunkumin zai tsanatwa Iran tare da hargitsa al’umarta, hakan zai sanya a fara yi wa gwamnati bore wanda dole a kifar d ita ko ta sauya manufofinta.

Turkiyya ta nuna adawa da rashin amincewa kan wannan takunkumi da aka saka wa Iran saboda Amurka jal tilo ce ta dauki wannan mataki. Turkiyya ce kasa ta biyu dake sayen albarkatun isakar gas daga Iran. A kowacce shekara Turkiyya na sayen kusan mitakyup biliyan 9.5 daga hannun Iran. Kuma ana hasashen wannan aksuwanci zai ci gaba. Alkaluman 2017 sun nuna cewa Turkiyya na kan gawba a tsakanin kasashen da Iran ke fitar da man fetur. Ana kuma ganin Turkiyya na iya karkata ga Iran kadai wajen sayen man fetur tare da barin wasu kasashe. Kuma nan wani lokaci Tyurkiyya na shirin aiwatar da yarjejeniyar kasuwanci da kudin gida da ta kulla da Iran. Haka kuma Turkiyya na shirin fara tsimi da tanai wajen man fetır din da take amfani da shi saboda gibin da za a iya samu a kasuwannin duniya.  

Idan muka kalli misalai kan abubuwan da suka gabata, takunkumi bai taba canja wata gwamnatin kama karya ba. A tasirhin siyasar kasa da kasa za a ga cewar an fana da amfani da takunkumin tattalin arziki da wuri. Amma kuma talkunkuman na iya zama matakin biyar bukatar masu saka shi a matkin farko. Ana ganin yadda a siyasar huldar kasa da kasa takunkumai ke rage karfin tattalin arziki na  kasashen da aka sakawa tare da gallazawa jama’a da jefa su cikin halin kaka nika yi. Kuma za a iya ganin yadda gwamnatocin da ake saka wa takunkumi suke kirkirar fahimtar an takura musu da jefa su cikişşn matsi inda suke jan shugabannin al’auma jikinsu ko kuma su hada karfin kasa da kasa don tunkarar wannan mataki da aka dauka a kansu. Abin takaici ne yadda takunkuman ke shafar jama’ar kasa talakawa kawai. Kuma wani babban abu mara kyau mai illa da irin wadannan takunkuman suke haifarwa shi ne kangararwa da kalaman tsaurin ra’ayi.  Akwai yiwuwar takunkumin da aka saka wa Iran ya haifar da irin wannan sakamako. Wannan zai sake saka Iran ta ci gaba da yada manufofinta a gabas ta Tsakiya ta kowacce hanya da za ta iya yin hakan.

A karshe, wannan takunkumi zai iya janyo rikici da matsaloli a tsakanin kasashen duniya. A bangaren tattalin arziki kuma, man fetur zai iya hauhawa tare da janyp tashin farashi a kasashen duniya da dama.Labarai masu alaka