Dare daya Allah kan yi Bature

Akalla ma'aikata 230 na wani kamfanin mulmula farin karfe na kasar Beljiyom ne suka yi kacibus da jimillar albashinsu na shekaru 25 a lokaci daya a asasunsu na banki ba tare da sun san hawa ko sauka ba.

A cewar kafar yada labaran kasar Burtaniya BBC,an dai zuba wadannan makudan kudaden a asusunsu ma'aikatan maimakon albashinsu,wanda Yuro 100 ne kacal a wata.

Yayin da wasu daga cikin ma'aikatan wadanda abun ya zo musu a matsayin bazata suka dinka shakku,wasu kuma tuni suka dinka kwasar ganima tare da biyan dukannin wasu basussukan da suka yi musu katutu, har ma da zuwa gidajen caca.

To sai dai tuni kamfanin ya farga da irin barnar da ta tafka,inda ya bukaci da a dawo ma sa da kudadensa kadaran-kadahan.

An sanar da cewa,kamfanin mulmula farin karfen na samun akalla Yuro dubu 600,000 a kowane wata. Labarai masu alaka