Takunkumi ga Iran da sakamakon da zai haifar

Bayan janyewar Amurka ƙarƙashin jagorancin Donald Trump daga yarjejeniyar nukiliyar Iran da ƙasashe 5+1 suka gudanar a lokacin mulkin Obama, ma'aikatan kuɗin Amurka ta kakkaɓawa lran takunkumai har sau biyu.

Takunkumi ga Iran da sakamakon da zai haifar

Bayan janyewar Amurka ƙarƙashin jagorancin Donald Trump daga yarjejeniyar nukiliyar Iran da ƙasashe 5+1 suka gudanar a lokacin mulkin Obama, ma'aikatan kuɗin Amurka ta kakkaɓawa lran takunkumi na farko a ranar 7 ga watan Agusta, bayan kwanaki 180 kuma ta sake kakkaɓawa ƙasar takunkumi karo na biyu a ranar 5 ga watan Nuwamba. Takunkumin Amurkan akan lran zasu shafi lamurkan makamashi, bankuna, sufuri da kanfunan inshora.

Takunkumin farko da Amurka ta kakkaɓawa lran ya kangeta daga samun dalar Amurka, sayar da ma'adanan gwamnati da kuma gudanar da cinikin zinari, ƙarafa da makamantansu har dama shigowa da kayayyakin jiragen sama. Takunkumin na biyu kuma zai shafi lamurkan fitar da man fetur da iskar gas da suka kasance ƙashin gwiwar tattalin arzikin kasar.

Ɗaya daga cikin muhimman abubuwa da suka kasance sahun gaba akan janyewar shugaban Amurka Donald Trump ya yiwa ƙasarsa ita tilo daga yarjejeniyar nukiliyar Iran ita ce tsarin musayar kuɗaɗen SWlFT tsakanin bankunan ƙasa da ƙasa. Bayan takunkumin Amurka akan lran cibiyar SWlFT ta fitar da sanarwar cewa ta toshe lran daga iya fa'idantuwa da tsarin. Haka kuma takunkumin ta ƙunshi hukumomin kuɗaɗen ƙasa da ƙasa, sabili da takunkumin zai rage ƙarfin babban bankin kasar Iran da kuma ma kanfunan harkokin kuɗaɗe a ƙasar. Bugu da ƙari takunkumin zai sanya kanfuna da wasu ƴan ƙasar lran 700 cikin bakar littafi kamar yadda ma'aikatan kuɗaɗen ƙasar Amurka ta sanar.

Duk da irin takunkumin da aka kakkaɓawa lran, mai bada shawara akan lamurkan tsaro a fadar White House John Bolton ya bayyana cewar za'a sake kakkaɓawa lran takunkumi fiye da wandanda aka kakkaɓa mata a halin yanzu, inda ya ƙara da cewa takunkumin da za'a kakkaɓawa lran a halin yanzu ba zai tsaya kamar irin na wadanda aka yi a lokacin mulkin Barack Obama ba.

A lokacin da aka kakkaɓawa lran takunkumin an bayyana ƙasashe 8 da suka haɗa da China, lndiya, ltaliya, Girka, Turkiyya da wasunsu da takunkumin ba zai shafa ba, a kan hakan ne shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewar wannan takunkumin gaba dayanta bata dace ba. Erdoğan ya ƙara da cewa a gurinmu takunkumi mataki ne da zai gurɓata tsarin duniya. Kuma lamarin ne daya saɓawa dokar ƙasa da ƙasa da ma ƙaidar diflomasiyya. Muna da bukatar zama cikin tsanaki, ba jari hujja ba, muna fatan kasancewa cikin daidaito ba hakincewa ba, bai kamata mu kasance cikin yanayin da duk wanda ya samu dama zai gudanar da abinda yake so ba. Erdoğan ya ƙara da cewa idan muka duba Tarayyar Turai da ƙasashenta sun ƙalubalanci wannan takunkumin, hakan na nuni da irin yadda takunkumin keda fuskoki daban daban.

A yayinda  shugaba Recep Tayyip Erdoğan ke sharhi akan shigowa da kayayyakin makamashi daga lran ya bayyana cewar matsayinmu akan takunkumi a bayyane take, a cewar sa, mun sha bayyana matsayinmu akan wannan takunkumin musamman a lamurkan man fetur, tabbas ba zamu mutunta wannan takunkumin ba. Ya ƙara da cewa muna siyar iskar gas har na mitakup biliyan 10 daga gare ta, idan bamu siya ba a lokacin sanyi zamu sanya ƴan ƙasarmu cikin tsananin sanyi ne? Ba zamu mutunta wannan takunkumin ba, babu ruwan mu da ita.

Haka kuma, ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya bayyana cewar takunkumin da Amurka ta kakkaɓawa lran ya sabawa ka'ida, kuma ya sabawa ka'idodin majalisar tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya ƙarara. Bugu da ƙari, Faransa, China da Jamus sun fito fili inda suka soki lamarin, sai dai kasancewar dama, ƙarfi da ikon da Amurka keda shi a faɗin duniya ya sanya wasu muhimman kanfunan ƙasashen da suka ƙalubalanci yunkurin bayyana cewar zasu mutunta takunkumin.Labarai masu alaka