Iran ta ce ba ruwanta da takunkumin da Amurka ta saka mata

Shugaban Kasar Iran Hassan Ruhani ya bayyana cewar kasarsa ba ruwanta da takunkumin da Amurka ta ce ta saka mata inda za ta ci gaba da sayar da albarkatun man fetur ga kasashen waje.

A sanarwar da Ruhani ya yi a kafar yada labarai ta talabijin ya tabo batun takunkumin da Amurka ta saka musu wanda ya fara aiki a ranar litinin din nan.

Ruhani ya ce Amurka na son hana su sayar da man fetur gaba daya, za su ci gaba da sayarwa kuma ba ruwansu da takunku8min na Amurka.

A watan Mayu ne Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya bayyana fitar da kasarsa daga yarjejeniyar Nukiliya da aka kulla da Iran a shekarar 2015 inda ya ce, zai saka mata takunkumai a bangaren makamashi da sha'anin kudi.

Da m,salin karfe 6 na safe agogon Najeriya na ranar Litinin din an 5 ga Nuwamban 2018 takunkumi ya fara aiki.Labarai masu alaka