Turkiyya da Pakistan zasu fara kasuwancin bai daya

Shugaban kasar Pakistan Arif Alvi ya bayyana cewar nan bada jimawa kasarsa da Turkiyya zasu rataba hannu akan yarjejeniyar kasuwancin bai daya da juna.

Alvi ya yi sharhi ne a yayinda yake jawabi a taron baje kolin hukumar kasuwancin kasar Pakistan, Inda ya jaddada cewa kasarsa zata kulla hurdar kasuwanci da Turkiyya.

A lokacin da Alvi ya ziyarci Istanbul ya gana da shugaba Recep Tayyip Erdoğan inda suka tatauna akan lamurkan kasuwancin kasashen biyu.

Alvi, ya kara da cewa nan bada jimawa ba Turkiyya da Pakistan zasu fara kasuwancin bai daya domin inganta lamurkan kasuwanci da tattalin arzikin kasashen biyu.

Ya kara da cewa kanfunan Turkiyya 4 za su saka hannayen jari har na rabin dala biliyan a kasar pakistan

Shugaban kasar Pakistan  Alvi ya ziyarci Turkiyya domin bukin zagayowar ranar kafa Turkiyya 29 ga watan Oktoba da kuma bude sabon filin tashi da saukar jiragen sama ta Istanbul, inda ya gana da shugaba Recep Tayyip Erdoğan.

 Labarai masu alaka