Tattalin arzikin Turkiyya na ci gaba da habaka

A makon jiya alƙaluman da aka fitar dangane da hauhawan farashin kayyayaki a ƙasar Turkiyya sun bayyana cewar, a yayinda alƙaluman farashin masu sayen kayayyaki yake 24.5, alƙaluman farashin masu sayar da kayayyakin yakai 46.1.

Tattalin arzikin Turkiyya na ci gaba da habaka

        

A makon jiya alƙaluman da aka fitar dangane da hauhawan farashin kayyayaki a ƙasar Turkiyya sun bayyana cewar, a yayinda alƙaluman farashin masu sayen kayayyaki yake 24.5, alƙaluman farashin masu sayar da kayayyakin yakai 46.1. Wadannan alƙaluman sun kasance masu yawan da aka taɓa samu tun a shekarar 2003, wannan tashin farashin kayyayakin na makon jiya ya nuna cewa a cikin shekaru 15 dinnan an samu hauhawar farashin da ba'a taba samun irin sa ba. Hakika, baya ga matsalolin cikin gida, muna sane da akwai wadansu kalubalolin da suka haifar da hakan.

Tabbas, baƙadalar harkokin canji da aka kirkiro wa ƙasar a watan Agusta shi ne babban dalilin da ya sanya tashin gworon zabbin farashin kayayyaki a ƙasar. A yayinda ake hasashen wannan kutingwilar dake faruwa a kasuwar canjin ka iya ci gaba da kuma ƙara haifar da rashin daidaito da tsanaki a kan farashin kayyayaki ya kamata mu yi sharhi akan lamarin. Da farko dai ya kamata mu yi tambaya akan shin ko wasu irin matakai za'a iya dauka domin kange wadannan iftila’in da suke kokarin daƙile ci gaban da tattalin arzikin Turkiyya ke samu? Shin ko wasu abubuwa suka wajaba akan al'ummar ƙasar Turkiyya dama kanfunan ƙasar domin yaƙar wannan hauhawan farashin kayyayakin baki ɗaya? 

Turkiyya ta jima tana fuskantar matsalolin tashin farashin kayyayaki. A shekarar 2002 lokacin da jam'iyyar AK Parti ta hau ragamar mulki, farashin kayyayaki a ƙasar yana kashi 60 cikin ɗari. A cikin shekaru 16, sabili da ƙwararan matakai da aka dauka farashin kayyayaki ya sauka da dama. Daga shekarar 2002 zuwa yau, Turkiyya bawai matakan siyasa da tattalin arziki kawai ta dauka ba, ta kuma kula da lamurkan hauhawan farashin kayayyaki domin inganta rayuwarwar al'ummar ƙasar.Amma bayan yunƙurin juyin mulki a shekarar 2016 an dauki matakan ƙalubalantar siyasa da tattalin arzikin Turkiyya ta hanyar dagule harkokin canji a ƙasar da ya fara haifar da hauhawan farashin kayayyaki a halin yanzu.

A yau dai, tun daga sabbin tsarukan tattalin arzikin da aka ƙaddamar, ya ɗoru akan wuyar kowa ya ɗaura ɗamarar yaƙar hauhawan farashin kayyayaki. Tabbas, dagule lamurkan canjin da ake yi a ƙasar ya shafi kowa, saboda haka ya zama wajibi akan dukkanin al'ummar ƙasar su dauki matakin daidaita lamurkan tattalin arziki kamar yadda suke a da.

Kamar dai yadda muka sani, hauhawar farashin kayyayaki, tashin canji da riba lamurka uku ne da ya kamata a nisanta su daga tattalin arziki. Ɗaukar matakan daidaita harkokin canji ta hanyar ƙara riba; bai da wata fa'ida ga tattalin arziki idan aka yi la'akari da dogon zango, haka kuma baida wata kataɓus da zai ƙara ga lamurkan saka hannun jari.

Domin dai-daita tattalin arzikin Turkiyya ya kamata a nisanta ta daga waɗancan ababe uku da muka ambata. Ƙara riba baida wata alfano da ake tunanin za'a iya samu, haka kuma wannan ba mataki ne da zai inganta harkokin saka hannayen jari ba.A cikin wannan yanayin akwai bukatar a dauki matakan magance tashin farashin kayyayaki ta ko wacce fani, sabili da tashin farashin kayyayaki ka iya haifar da rage sayen kayayyaki a cikin ƙasar.

Haƙiƙa, hauhawan farashin kayyayaki ba lamari ne da za'a sanya ma ido ba a cikin ƙasa. Saboda haka ya zama wajibi a dauki ƙwararan matakai da kuma ƙarfafa matakan da zasu inganta lamurkan cikin gida baki ɗaya.

Akan wannan lamarin; ya tilastu ga ma'aikatun gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu dama kanfunan ƙasar su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin magance tashin farashin kayyayaki a kasar, da irin wannan yunƙurin ne za'a iya dakatar da kauda yiwuwar ci gaba da hauhawan farashin kayyayaki iri daban daban. A yau dai; muna da tabbacin cewa matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu, za'a kawo karshen su cikin ɗan ƙanƙanen lokaci, kuma tattalin arzikin kasar Turkiyya zai cigaba da bunƙasa a koda yaushe.Labarai masu alaka