Amurka ta bayyana niyyarta na yin sabuwar yarjejeniya da Iran

Wakilin Amurka na musamman kan Iran Brian Hook ya bayyana cewa, suna son sanya hannu kan yarjejeniyar samar da makamai masu linzami, karin kan yarjejeniyar Nukiliya.

Hook ya ce "Fatanmu shi ne yin sabuwar yarjejeniya da Iran. Ba wai san rai suke so ba, yarjejeniya suke so tsakanin kasashe 2. Yarjejeniyar Nukiliya da aka yi da Iran ba yarjejeniya ba ce. Majalisar Dattawan Amurka ba ta jefa kuri'ar amincewa da ita ba. Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ne kawai ya jefa kuri'a, a saboda hakaidan ana son abu mai inganci kuma dauwamamme dole sai an yi yadda muke so."

Hook ya kuma ce, kan wannan batu suna ci gaba da aiyuka tare da China da Rasha.

Ya ce "Sabuwar yarjejeniyar da za a yi za ta shafi makamai masu linzami, ba wai sarrafa Nukiliya kawai ba."Labarai masu alaka