Jirgin sama na farko da Turkiyya ta samar ya fara tashi

Jirgin sama mai saukar ungulu na farko da Turkiyya ta samar samfurin T625 da ake iya yin kowanne aiki da shi ya fara tashi.

Jirgin sama na farko da Turkiyya ta samar ya fara tashi

Jirgin sama mai saukar ungulu na farko da Turkiyya ta samar samfurin T625 da ake iya yin kowanne aiki da shi ya fara tashi.

Shugaban Hukumar Kula da Masana'antun Kayan Tsaro na Turkiyya Isma'il Demir ya ce, jirgn da aka samar da shi da kayan cikin gida ya fara tashi.

Jirgin na T625 yana iya tashi a yanayi mummuna, yana tashi sama sosai, yana iya aiki a karkashin tsananin zafi kuma dare da rana yana.

Jirgin yana da siffofin daukar kaya, yana iya zama na daukar marasa lafiya, na aiyukan ceto da sauka a gabar teku.

Jirgin na da wajen matuka 2 da fasinjoji 12 kuma ana sa ran fitar sa kasuwannin duniya a shekarar 2021.

 Labarai masu alaka