Siyasar Tattalin Arziki

Ganin yadda tattlin arzikin Turkiyya ke ƙara tsayi da gindinsa duk da irin baƙadalan da yake fuskanta a cikin ƴan kwanakin nan na karantar da irin fa'idan da tattli da tanadi ke da shi ga tattalin arzikin ƙasa.

Siyasar Tattalin Arziki

Sabili da maƙullin bunƙasar tattalin arzikin ƙasa shi ne tattli da tanadi ya sanya duk yadda aka ƙalubalanci tattalin arzikin Turkiyya za ta iya magance lamarin cikin ƙanƙanen lokaci. A ɗaya barayin kuma, Turkiyya wacce ke ɗaya daga cikin ƙasashe masu tasowa, idan bata tanadi ba zata iya shiga cikin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki ba. Haƙiƙa ci gaba da bunƙasar da kuɗaɗen shigar manyan ƙasashen duniya ke ci gaba da yi nada nasaba da muhimmanci ga irin tsarin tattali da tanadin da suke dashi.

A yau babban dalilin da ya sanya rashin bunƙasar tattalin arzikin kasashe masu tasowa shi ne rashin tattali da tanadi. Sabili da haka, akwai bukatar yin tanadi domin ci gaba da bunƙasar tattalin arzikin ƙasa. Tattali da tanadi dai sun kasance ƙashin gwiwar bunƙasar tattalin arzikin ƙasa.

Sai dai a hakikanin gaskiya, wannan tanadin na da bukatar kuɗaɗe da dama domin ba zai yiwu ga kasashe masu rashin yawan kuɗaɗen shiga ba, sabili da haka akwai bukatar ƙasashe su nemi yadda zasu bunƙasa kuɗaɗen shigar su, bayan haka su kuma kauracewa bashin da suke karɓa daga ƙasashen waje.

Tsimi da tanadi ga ƙasa yakan rage mata yawan dogaro ga kasashen waje da kuma inganta tattalin arzikinta. Hakan nada muhimmanci sosai a fagen samawa tattlin arzikin ƙasa ƴanci.

ldan muka dubi tanadin manyan ƙasashe dangane da kuɗaɗen shigar su zamu ga yana gwaɓi sosai. Zamu iya kwatanta misali ga Jamus wacce ƙarfin tattalin arzikinta ya ta'allaka ga irin tsimi da tanadin da take yi a koda yaushe.

A takaice, a yau Amurka ta ƙaddamar da yaƙin tattalin arziki a fadin duniya domin kare tattlin arzikinta, inda take amfani da nau'in kuɗin dala domin sakawa kasashe takunkumi kasancewar hakincin da dalar ta samu a hada-hadar kasuwanci a duniya.

 A wannan yanayin, kasashe masu tasowa nada bukatar kara maida hankali akan tsimi da tanadi domin kaucewa duk wata ƙalubale da kuma ƙara gina tattlin arzikinsu a koda yaushe.Labarai masu alaka