Wani Limami dan kasar Masar zai sayar da gwala-gwalan matarsa don goya wa Turkiyya baya

Wani Limami dan kasar Masar dake rayuwa a Kuwait ya bayyana cewa, zai sayar da kayan ado na matarsa don taimaka wa Turkiyya da kudin.

turkiye destek.jpg

Wani Limami dan kasar Masar dake rayuwa a Kuwait ya bayyana cewa, zai sayar da kayan ado na matarsa don taimaka wa Turkiyya da kudin.

Dan kasar ta Masar da ke Limanci a Kuwait Seyyid Muhammed Mustafa ya je ofishin jakadancin Turkiyya da ke Kuwait inda ya ce, ya zo ne don ya bayar da kyautar gwala-gwalan matarsa ga Turkiyya saboda irin kullalliyar da aka shirya mata.

Da aka tambaye shi me ya sa ya ke son yin haka sai Mustafa ya ce, "saboda irin son da na ke yi wa 'yan uwana Turkawa. Ku ne farin cikin Musulmi a yau."

Ya ce, yana kaunar Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan sosai kuma yana yi masa addu'a a koyaushe.

Liman Mustafa ya yi kira ga Turkawa da su san kimar Shugaba Erdogan.

Mataimakin jakadan Turkiyya kan aksuwanci Atilla Ugur ya bayyana cewa, Mustafa da ya so taimaka wa Turkiyya ya yi tunani mai kyau kuma ba za su karbi wannan taimakon ba.

Sakamakon haka Mustafa ya ce, daga yanzu zai sayi kudin Turkiyya kuma kayan da aka samar a Turkiyya zai dinga saya.Labarai masu alaka