Turkiyya ta gargadi Amurka game da saka mata takunkumi

Turkiyya ta gargadi Amurka inda ta sanar da cewa,za ta yi ramuwar gayya kan takunkumin da Amurkan ta saka mata.

Turkiyya ta gargadi Amurka game da saka mata takunkumi

Turkiyya ta gargadi Amurka inda ta sanar da cewa,za ta yi ramuwar gayya kan takunkumin da Amurkan ta saka mata.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Kasar Hami Aksoy ya bayar da amsar tambayar da aka yi masa bayan aike wa da sakon Twitter game da ninka harajin da Donald Trump ya saka wa Turkiyya kan bakin karfe da alminiyom da ta ke shigarwa da shi Amurka.

A amsar tasa Aksoy ya ce, Trump ya yi burus da dokokin Kungiyar Kasuwanci ta Duniya inda ya kara yawan haraji kan bakin karfe da alminiyom da Turkiyya ke shigarwa da shi kasarsa wana hakan bai da ce ga gwamnatinsa ba. 

Ya ce ya kamata Trump ya san cewa, wannan abu ba zai amfani hadin kan kasashen ba, kuma zai kawo cikas da nakasu game da kawancensu. 

Kakakin ya ci gaba da cewa, kamar kowanne lokaci Turkiyya za ta mayar da martani kan wannan mataki da amurka ta dauka, kuma Turkiyya na kasancewa a aiyukan warware rikici ta hanyar sulhu, diplomasiyya, tattaunawa da kyakkyawar niyya.Labarai masu alaka