Erdogan ya bukaci Turkawa da su canja kudaden kasashen waje zuwa kudin kasa

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa, Turkiyya ba za ta yi rashin nasara a yakin tattalin arzikin da ake yi ba.

Shugaban na bayani ne game da hawa da kudaden kasashen waje suke yi kan kudin Turkiyya Lira.

A ziyarar da ya kai Bayburt Shugaba Erdogan ya bukaci jama'a da su canja kudaden da suke da su zuwa Lira domin bayar da amsa ga Yammacin duniya.

Ya kara da cewa, ba za su yi rashin nasara ba a yakin tattalin arziki da ake yi a yau.Labarai masu alaka