An yanka ta tashi tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa

Koriya ta Arewa ta gargadi wasu Shugabannin Amurka da ke sake yin kira da a kara wa kasar takunkumai a matakin kasa da kasa inda ta ce, yin hakan zai iya dakatar da yunkurin da ake yi na yaki da mallakar makaman Nukiliya.

Kamfanin dillancin labarai na Yonhap ya rawaito na Koriya ta Arewa KCNA wanda ya bayar da bayanan Shugabannin Koriya ta Arewan da suka bayyana daina gwada harba makaman Nukiliya tare da rushe wajen da ake samarwa da harba makaman na sake yin barazana da cewa, matukar wasu 'yan siyasar Amurka za su ce a kara musu takunkumai to lallai za a kawo cikas a kokarin hana mallakar Nukiliya.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Koriya ta Arewa ya ce a karkashin yarjejeniyar da Amurka ta kulla da Koriya ta Arewa ta tanadi hadin kai tare da aiki tare, amma kuma idan aka nuna halayya sabin haka to lallai kar a sa ran za a samu natijar hana su mallakar Nukiliya.

 Kakakin da ba a bayyana sunansa ba ya kuma kara da cewa, babu tabbas din zaman lafiyar da aka sha wahala wajen samun sa a tsibirin Koriya zai dore.

A makon da ya gabata Ministan Harkokin Wajen Koriya ta Arewa Ri Yong Ho ya soki yadda Amurka ke ci gaba da kakaba musu takunkumi duk da irin kyakkyawar niyyar da suke da ita wadda suka bayyana ta karara ga duniya.

Ministan Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya yi kira ga rasha da sauran Kasashen duniya da kar su saba ka'idar takunkuman daka saka wa Koriya ta Arewa.Labarai masu alaka