Wata sabuwar Annoba na hallaka dabbobi a lran

Ɗan majalisa mai wakiltar Bem a ƙasar lran Habibullah Nikzadipenah ya bayyana cewar annobar cutar dabbobi ta halaka dabbobi 70 a jihar Kirman dake ƙasar.

Wata sabuwar Annoba na hallaka dabbobi a lran

Ɗan majalisa mai wakiltar Bem a ƙasar lran Habibullah Nikzadipenah ya bayyana cewar annobar cutar dabbobi ta halaka dabbobi 70 a jihar Kirman da ke ƙasar.

Nikzadipenah dake jawabi ga kanfanin dillancin labaran majalisar ya bayyana cewar a filin Habr Park dabbobi 70 da suka haɗa da raguna da sauran dabbobi 70 sun hallaka.

Nikzadipenah da ya bayyana cewar annobar nada nasaba da dabbobin dake shigowa ƙasar daga ƙasashen waje, inda ya ƙara da cewa in ba'a ɗauki mataki ba hakan zai shafi sauran dabbobin ƙasar.

Ya ƙara da cewa, shekaru 20 kenan da jihar ke fama da fari lamarin da ya sanya rashin ishesshen ruwa dake ƙara jefa dabbobin daji dana gida cikin haɗari.

 Labarai masu alaka