Shugabannin Iran sun zargi Amurka da yunkurin hargitsa musu Kasa

Mataimakin Shugaban Kasar Iran na farko Ishak Jihangir ya bayyana takunkumin da Amurka ke saka wa kasarsa a matsayin yunkurin hargitsa kasar tare da janyo rikici.

Jihangiri ya yi jawabi a jihar Isfahan inda ya ce, Amurka na hada kai da Saudiyya wajen aiyukanta.

Ya ce, sun shirya don tunkarar dukkan abinda ka iya zuwa ya komo.

Jihangir ya kuma tabo batun da hana sayen man fetur a wajensu da Amurka ke yi inda ya ce, da Yardar Allah Amurkawa ba za su iya dakatar da fitar da man fetur da Iran ke yi ba. Iran za ta nuna matakan da ta dauka a wannan shekarar.

Ya kuma kara da cewa, daga cikin shirinsu har da sayar da man fetur din a kasuwar cikin gida.Labarai masu alaka