Turkiyya za ta fara kera motoci masu aiki da wutar lantarki

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewar mota mai aiki da wutar lantarki da kasar Turkiyya za ta kera a shekarar 2021 zai samar da dala biliyan 50 ga kudin shigar kasa.

Shugaba Erdoğan da ya yada a shafinsa ta twitter ya kara da cewa Turkiyya za ta fara kera motoci da za suyi aiki da wutar lantarki domin rage dogaro ga man fetur.

Turkiyya na shirin bunkasa lamurkan kasarta har guda 100 da suka hada da kimiyya, fasaha da kere-kere. 

Daga shekarar 2002 zuwa yau an samu karuwar fitar da kayyakin motoci har sau 6. A yayinda a 2002 ake fitar da kayyayakin motoci na dala biliyan 4.8 a shekarar 2017 ya haura 28.5. Haka kuma a 2002 ana kyera motoci dubu 347 a 2017 ana kyera dubu miliyan daya da dubu 696 dake nuna karuwar 4.8cikin dari. Labarai masu alaka