Najeriya da Morokko sun sanya hannu kan yarjejeniyar cinikayyar albarkatun iskar gas

Mai taimakawa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan kafafan yada labarai Malam Garba Shehu ya bayyana cewa, kasar tare da Morokko sun sanya hannu kan yarjejeniyar cinkayyar iskar gas.

Shehu ya ce, an sanya hannu kan yarjejeniyar a lokacin da Buhari ke gana wa da Sarkin Morokko Muhammad na 6 a yayin da ya ziyarci Morokko.

Sanarwar da Shehu ya fitar ta kara da cewa, Najeriya da ke fitar da albarkatun iskar gas ga kasashen yankin Sahara, a yanzu za ta fara kai shi Turai ta hanyar shimfida bututu da zai bi ta Morokko.

Ya ce, bututun na da tsayin kilomita dubu 5,600.

Wannan aiki dai zai samar da aiyukan yi ga matasan Kasar.Labarai masu alaka