Pakistan za ta sayi jiragen yaki 30 daga hannun Turkiyya

Dakarun Turkiyya sun fara fitar da jiragen sama masu saukar ungulu da kamfanin samar da makamai na Turkiyya ya kera don amfanin sojojin Kasar.

Pakistan za ta sayi jiragen yaki 30 daga hannun Turkiyya
Turkiyya ta amince da sayarwa Pakistan jiragen yaki masu saukar ungulu samfurin ATAK
Turkiyya ta amince da sayarwa Pakistan jiragen yaki masu saukar ungulu samfurin ATAK

Turkiyya ta amince da sayarwa Pakistan jiragen yaki masu saukar ungulu samfurin ATAK

Dakarun Turkiyya sun fara fitar da jiragen sama masu saukar ungulu da kamfanin samar da makamai na Turkiyya ya kera don amfanin sojojin Kasar.

Daga shekarar 2015 zuwa yau an mika wadakarun soji da na Jandarma na Turkiyya jiragen sama na yaki samfurin ATAK guda 35 wadanda ake kuma ci gaba da yaki da ta'addanci da su.

Atak na daga cikin kayan yaki da suka fi jan hankali a duniya wadanda Turkiyya ta samar kuma a yanzu an fara fitar da jiragenzuwa kasashen waje. An samu sakamako mai kyau kan tattaunawar da ake yi da Pakistan kan sayar musu da Atak.

Pakistan za ta sayi jiragen na Atak har guda 30 daga hannun Turkiyya inda kasashen 2 suka sanya hannu kan yarjejeniyar cinikin.

A ranar 23 ga watan Maris ne aka gudanar da gwajin jiragen a wajen bikin ranar tsaro ta Pakistan.

Tag: Atak , Turkiyya

Labarai masu alaka