Turkiyya ta fara yin duk maganin da take bukata a cikin gida

Firaministan Turkiyya Binali Yıldırım ya bayyana cewar Turkiyya ta fara yin kusan duk maganin da take bukata a cikin gida, inda ta fara sayar da magani har na milyoyin Lira zuwa kasashen waje.

Ayayinda a shekarar 2017 Turkiyya ke yin kashi 80 cikin darin maganin da take amfani dashi, a halin yanzu kusan dukkanin maganin da za'a yi amfani dasu a kasar ana yin sune cikin gida. Hakan ya bata damar sayar da magani na Lira biliyan 2.2, a yayinda take yunkurin cimma aniyar sayar da magani zuwa kasashen waje har na lira biliyan 6.1

Za'a kuma dunga kera sauran kayyayaki da na'urorin asibiti, lamarin da zai samar da cinikin lira biliyan 6.

Yıldırım ya kara da cewa, Turkiyya zata dauki dukkan kwararan matakai domin cimma burinta na kera kusan dukkan kayayyakin da take bukata a cikin gida, hakan zai bunkasa tattalin arzikin kasar ta hanyar inganta kasuwanci da sauran kasashe.

 Labarai masu alaka