Bincike: Ana biyan maza albashi fiye da mata a Nahiyar Turai

An bayyana cewar mata a Nahiyar Turai na samun kudin shiga kasa da maza da kaso 16 cikin dari.

Bincike: Ana biyan maza albashi fiye da mata a Nahiyar Turai

An bayyana cewar mata a Nahiyar Turai na samun kudin shiga kasa da maza da kaso 16 cikin dari.

Kamar yadda hukumar kididdigar Eurostat ta bayyanar, alkaluman shekarar 2016 sun tabbatarda a duk lokacin da namiji ya samu Euro daya mace na samun cent 84 ne.

Sakamakon binciken ya tabbatar da anfi samun ire-iren wannan rashin dai-daiton kudin shiga tsakanin mata da maza a kasashen Jamus da Ingila.

A wadannan kasashe ana biyan maza albashi fiye da mata da kaso 21 cikin dari.

A dayan barayin kuma, a yayinda a  kasashen Romaniya, Italiya da Luxsemburg babbancin yake da kashi 5 cikin dari, a Faransa yakai 14 cikin dari.

 Labarai masu alaka