Saudiyya ta janye dokar muharami ga mata 'yan sama da shekaru 25

Kasar Saudiyya ta bayyana cewar za ta fara baiwa mata 'yan sama da shekaru 25 damar shiga kasar ba tare da muharami ba.

Saudiyya ta janye dokar muharami ga mata 'yan sama da shekaru 25

Kasar Saudiyya ta bayyana cewar za ta fara baiwa mata 'yan sama da shekaru 25 damar shiga kasar ba tare da muharami ba.

Shugaban hukumar yawon bude idon kasar Omar Al- Mubarak ya bayyana cewar domin kara habbaka lamurkan yawon bude idon, kasar Saudiyyar za ta janye dokar muharrami ga mata da su ka fiye shekaru 25.

Mubarak ya kara da cewa visar da za'a baiwa matan ba za ta wucce na kwanaki 30 ba.

Wannan matakin nada nasaba ga irin matakan da yarima Muhammed Bin Salman ke dauka domin bunkasa tattalin arzikin kasar ta hanyar habbaka fannonin bude ido, da kuma yin kwaskwarima ga addinin Wahhabism na tsattsaurar ra'ayi.

Baya ga garin Makka da Madina za'a kuma baiwa baki 'yan yawon bude idon damar yin aiki a fadin kasar Saudiyyar.

Za'a kuma fara gina wani katabaren gurin shakatawar kasa da kasa a cikin wasu hamada 50.

Haka kuma ana hasashen za'a kammala ginar yankin 'yancin da za'a dinga amfani da dokar kasa da kasa maimakon shari'ar musulunci a shekarar 2022 a kasar.

 Labarai masu alaka