Morokko ta harba tauraron dan adam mallakarta zuwa duniyar sama

Gwamnatin Morokko a ranar Larabar nan taharba tauraron dan adam zuwa duniyar sama da nufin karfafa harkokin leken asiri da yaki da ta'addanci.

An harba tauraron mai suna "The Mohammed VI-A satellite" daga tashar harba taurarin dan adam ta Faransa da ke Kourou a kan makamin roka samfurin Vega.

Za a iya amfani da tauraron wajen leken asiri tare da gano mafaka da maboyar 'yan ta'adda a iyakokin kasar ta Morokko.

A shekarar 2018 ma gwamnatin Morokko za ta sake harba wani tauraron na dan adam zuwa sama.

Morokko ce kasa ta 3 a Afirka da ta harba tauraron dan adam mallakarta bayan Masar da Afirka ta Kudu.Labarai masu alaka