ILO: Mutane sama da miliyan 201 ne ba su da aiyukan yi a duniya

Kungiyar Kwadago ta Kasa da Kasa ta fitar da rahotonta na rashin aikin yi na shekarar 2017.

ILO: Mutane sama da miliyan 201 ne ba su da aiyukan yi a duniya

Kungiyar Kwadago ta Kasa da Kasa ta fitar da rahotonta na rashin aikin yi na shekarar 2017.

Rahotan na bana ya bayyana cewa, Kanana da Matsakaitan Sana'o'i sun taka rawa sosai wajen samar da aiyukan yi a duniya.

An bayyana cewa, a tsakanin shekarun 2003 da 2016 yawamn masu aiki na cikakkiyar rana a bangaren kanana da matsakaitan sana'o'i ya ninka sama da sau 2. 

Aiyukan da wannan bangare ya samar a kasashe masu taso wa ya kama kaso 52 cikin 100 inda a kasashen da suka ci gaba kuma ya tashi kaso 41.

Kungiyar ta ce, a shekarar 2017 rashin aikin yi a duniya ya karu da kaso 5.8 inda ta yi gargadin cewa, wannan abu ba zai ragu nan da wani dan lokaci ba.

Haka zalika adadin mutanen da ba su da aikin yi a duniya baki daya ya haura miliyan 201 inda idan aka kwatanta da na shekarar 2016 za a ga ya dadu da miliyan 3.4.

Rahoton ya ce, a shekarar 2016 an aikatar da mutane biliyan 2.8 a fadin duniya.Labarai masu alaka