Rasha ta janye yarjejeniyar sayan man fetur daga hannun Gwamnatin Kurdawan Arewacin Iraki

Daraktan Kamfanin sarrafa albarkatun man fetur na Gazprom mallakar kasar Rasha Mai Kula da Harkokin Gabas ta Tsakiya Sergey Petrov ya bayyana cewa kamfanin nasu ya fasa aikin tonar mai albarkatun mai a rijiyar Halepçe da ke yankin Kurdawan Arewacin Iraki.

Rasha ta janye yarjejeniyar sayan man fetur daga hannun Gwamnatin Kurdawan Arewacin Iraki

Daraktan Kamfanin sarrafa albarkatun man fetur na Gazprom mallakar kasar Rasha Mai Kula da Harkokin Gabas ta Tsakiya Sergey Petrov ya bayyana cewa, kamfanin nasu ya fasa aikin tonar mai albarkatun mai a rijiyar Halepçe da ke yankin Kurdawan Arewacin Iraki.

Petrov ya tattauna da 'yan jaridar rasha inda ya ce, sun fasa aikin saboda wahalar isa ga rijiyar sannan kuma akwai yiwuwar samun ababan fashe wa da aka binne a yankin.

Darakta Petrov ya kara da cewa, rijiyar mai ta Halepçe na waje mai tudun mita dubu 2. Sakamakon yadda aka samu rikici a yankin ya sanya akwai bama-bamai da aka binne a kasa.  Akwai bukatar zuba jari mai yawa idan ana so yin aiki tukuru. Kuma wadannan suna da hadari sosai. Saboda haka ba za mu yi aikin ba."Labarai masu alaka