Sufurin jiragen sama na bunkasa a Turkiyya

Firaministan Turkiyya Binali Yıldırım ya bayyana cewa yadda harkokin sufurin jirgin sama ke habbaka a Turkiyya, kasar nasa ka iya zama cibiyar harkokin sufurin jiragen sama na duniya.

 Yıldırım, yayi wannan kalaman a lokacin da yake bude baki da 'yan kasuwar kasarsa a filin jirgin saman Istanbul na ukku da ake ginawa.

Ya kara da cewa filin zai kasance wani cibiyar mahadan duniya da zai dauki matafiya kimanin milyan 90 a Istanbul.

Firaministan ya kara da cewa duk da bunkasa Turkiyya na karuwa ne da kaso 6 cikin dari, harkokin sufurin jirgin sama daga 2002 yaci gaba da karuwa a ko wani shekara da kaso 15 cikin dari. Ana sufurin kimanin mutum milyan 33 dana cikin gida da waje. A yau dai hakkan yakai milyan 200. 

Binali Yıldırım ya kara da cewa wasu yankunan na kyashi ga yadda Turkiyya ke habbaka.

 Labarai masu alaka