Sojojin Venezuela sun fara atisayen nuna wa Amurka da kawayenta kwanji

Sojojin Venezuela sun fara wani atisaye na kwanaki 5 domin nuna wa Amurka da kawayenta dake yankin kwanji.

maduro tatbikat2.jpg
maduro tatbikat1.jpg

Sojojin Venezuela sun fara wani atisaye na kwanaki 5 domin nuna wa Amurka da kawayenta dake yankin kwanji.

Atisayen ya zo daidai lokacinda ake tarukan cika shekaru 200 da bayanan da jagoran kwatar 'yancin kasar daga Spaniya Simon Bolivar ya yi a Angostura.

Sakamakon atisayen an gudanar da bban taro sansanin soji na Guaicaipuro dake jihar Miranda wanda Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro da Ministan Tsaro Padrino Lopez tare da sauran manyan suka halarta.

A jawabin da Maduro ya yi ga sojojin ya bayyana manyan manufofin Simon Bolivar na kwatar 'yanci.

Ya ce, sojojin za su ci gaba da at,isayen har nan da ranar 15 ga Fabrairu domin nuna wa Amurka da kawayenta kwanji da kuma nuna musu kasar a shirye take game da duk wata barazana da za su yi musu.Labarai masu alaka