Zanga-Zanga ta sanya Macron fasa ziyartar kasashen waje

Sakamakon matsalolin da masu zanga-zanga dake sanye da riguna ruwan dorawa suka janyo a fadin kasar Faransa, Shugaban Kasar Emmanuel Macron ya soke ziyartar wasu kasashen waje da ya shirya yi har sai bayan 15 ga watan Maris.

Sanarwar da aka fitar daga Fadar Elysee ta ce, a kokarin shugaba Macron na warware matsalolin masu zanga-zangar ya fasa ziyartar kasashenw aje har sai bayan 15 ga watan Maris mai zuwa.

Sanarwar ta ce, an soke ziyartar garin Munich na kasar Jamus da Macron ya shirya yi  tare da sauran ziyarce-ziyarce a kasashen waje.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na sa ran gana wa da macron a wajen taron kan sha'anin tsaro a Munich.Labarai masu alaka