Trump: "Za mu sanar da mun gama yakar 'yan ta'addar Daesh"

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, akwai yiwuwar a mako mai zuwa su ayyana sun gama yakar kungiyar ta'adda ta Daesh a Siriya.

Trump ya ce "Ina so a jira sanarwa a hukumance."

Trump ya yi jawabi a wajen taron Ministocin Harkokin Kasashen Waje dake Yaki da Daesh wanda Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya halarta.

Trump ya yi bayanai game da irin kokarin da ya yi wajen yaki da Daesh tun bayan hawan sa mulki, kuma ana rantsar da shi ya bukaci Maaikatar Tsaro ta Pentagon da ta samar da wani tsari na yaki da Daesh gaba daya.

Trump ya ci gaba da cewa, a baya 'yan ta'addar Daesh na yin farfaganda a yanar gizo amma a yanzu babu su sam.

Trump ya kuma godewa kasashe da suka bayar da gudunmowa a yaki da 'yan ta'addar Daesh.Labarai masu alaka