Erdogan: Turkiyya ba ta taba samun matsala da Kurdawa ba

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya fadi cewar kasarsa ba ta taba samun wata matsala da al'umar Kurdawa ba.

Erdogan: Turkiyya ba ta taba samun matsala da Kurdawa ba

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya fadi cewar kasarsa ba ta taba samun wata matsala da al'umar Kurdawa ba.

Erdogan ya ce "Hada 'yan ta'addar PKK/PYD da al'umar yankunan da suke babban kage da sharri ne da za a iya yi wa 'yan uwanmu Kurdawa."

Shugaba Erdogan ya yi jawabi a lokacinda ya karbi bakuncin Kungiyar 'Yan Kasuwar Amurka da kuma Majalisar Hadin Kan Turkiyya-Amurka.

Ya ce "Alakar Amurka da Turkiyya ta ci dukkan wata jarrabawa tare da tsallake duk wani kokari na lalata ta."

Erdogan ya kara da cewar, Turkiyya da Amurka na da alaka mai karfi da muhimmanci. A wasu lokutan alakar na fuskantar matsalar sabanin ra'ayi amma kuma amma kuma hadin kan da kasashe ke da shi ya wuce a misalta.

Erdogan ya tabbatar da shirin Turkiyya na bayar da dukkan goyon baya tare da sauke nauyin dake kanta wajen yaki da 'yan ta'addar Daesh a lokacinda Amurka ta janye daga Siriya.

Shugaban ya bayyana sun fadi za su yaki Daesh gaba daya amma kuma sai aka hada kai da PYD/PKK wanda a nan gaba za a girbi wannan kuskuren da aka shuka.

Erdogan ya ce,Turkiyya na yaki da dukkan 'yan ta'addar da suke mata da ma duniya baki daya barazana.Labarai masu alaka