Trump zai gana da Kim Jong-un karo na biyu

Mai magana da yawun fadar gwamnati ta White House dake Amurka Sarah Sanders ta bayyana cewar a ƙarshen watan Fabrairu ne shugaban ƙasar Amurka Donald Trump da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong-un zasu tattauna karo na biyu.

Shugaba Trump ya gana da mataimakin shugaban jam'iyyar Workers Party ta Koriya ta Arewa Kim Yong-chol a faɗar White House.

Mai magana da yawun fadar gwamnati Sanders ta ƙara da cewa: "Akan yunkurin gudanar da taron kauda lamurkan makaman nukiliyar Koriya ta Arewa shugaba Trump ya gana da Kim Yong-un inda sunka tattauna har na tsawon awa daya da rabi.

Sanders, ta jaddada cewar taron da za'a bayyana inda za'a gudanar dashi daga baya, shugaba Trump na matuƙar fatan ganawa da shugaba Kim. 

Shugaba Trump ya yi ganawar farko da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong-un a ƙasar Singapore a ranar 12 ga watan Yulin shekarar bara inda anka aminta akan kauda lamurkan makamashin nukiliyar Koriya ta Arewa.

 Labarai masu alaka