Yadda Amurka ta damu da Isra'ila

Idan muka dubi salon siyasar Amurka a faɗin duniya, zamu ga cewa baya ga sukar da muke yi akan yadda matakanta suka saɓawa ƙa’idoji, tsarin siyasar na Amurka ya kasance ne akan ra'ayin wasu. Idan muka dubi tsarin siyasar Amurka a gabas ta tsakiya zamu ga

Yadda Amurka ta damu da Isra'ila

Idan muka dubi salon siyasar Amurka a faɗin duniya, zamu ga cewa baya ga sukar da muke yi akan yadda matakanta suka saɓawa ƙa’idoji, tsarin siyasar na Amurka ya kasance ne akan ra'ayin wasu. Idan muka dubi tsarin siyasar Amurka a gabas ta tsakiya zamu ga cewa matakan Amurkan da sukaa sabawa ƙa’idarta basu da wata alfano ga ƙasar dama al'ummarta baki ɗaya.

Shin ta wace hanya za'a iya cewa matakan da Amurka ta dauka ita tilo na mayarda ofishin jakadancinta na lsra'ila zuwa Ƙudus, sabanin ra'ayin dukkan ƙasashen duniya in banda wasu kaɗan a zaɓen da aka gudanar a Majalisar Ɗinkin Duniya zai iya amfanar da ƙasar?

Shin ko za'a iya gane ainihin manufar Amurka game da bayanan da ta fitar akan yankin cikin ƴan kwanakin nan?

Akan wannan sabuwar maudu'in mun sake kasancewa tare da ferfesa Kudret BÜLBÜL shugaban tsangayar ilimin siyasa a jami'ar Ankara Yıldırım Beyazıt.

Shin ko  sanarwar da Amurka ta fitar a ƴan kwanakin nan na nuni ga goyon baya ne ga kungiyar YPG wacce Turkiyya take kallo a matsayar ɓarayin kungiyar PKK wacce Amurkan ma ta aminta da ƴar ta'addace ?

Ƙalubalantar Turkiyya...

A ƴan kwanakin nan shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya ƙalubalanci Turkiyya inda ya bayyana cewar idan har ta kaiwa kungiyar YPG hari zai yiwa tattalin arzikin kasar giɓi.

Akwai bukatar a san da cewa  Turkiyya ba zata dauki ƙalubalantar Amurkan da wata muhimmanci ba;  ta ƙyale kungiyar ta'adda su dinga aikata ta'asa ba. Turkiyya ba zata sanya ido ta ƙyale yan ta'adda su kafa sansani su dinga gudanar da ayyukan kin kari a iyakokinta da yankunanta ba. Turkiyya zata iya watsi da dukkanin dangantakarta da Amurka ta kare kanta da iyakokinta daga maƙiya, zata iya sake ɗaukar matakan kauda ta'addanci a cikin dan kankanin lokaci.

Zamu iya sharhin cewa a halin yanzu Turkiyya ta canja ba kamar da ba.

Shin ko akwai wasu gyare-gyare ga kurakuren da Amurka ke tabkawa a Gabas ta Tsakiya?

Akan haka, babban abin tambaya anan shi ne, ko me yasa Amurka ke ɗaukar matakan da ba zasu amfanar da ita da kuma tattalin arzikinta ba a Gabas ta Tsakiya.

Misali, me ya sanya Amurka ɗaukar matakan da sunka saɓawa kusan dukkan ƙasashen duniya game da Ƙudus?

Turkiyya ta ɗauki dukkan matakan ƙalubalantar ɓarayin kungiyar ta'addar PKK a Siriya duk da irin haɗakar dake tsakanin ƙungiyar da kawarta Amurka, wacce dukkaninsu mambobin kungiyar NATO ne. Tamkar sauran ƙasashen NATO Turkiyya ta kasance a shafi daya wajen ƙalubalantar lamurkan ta'addanci.

Ko me ya sanya Amurka ke furta kalaman dake nuna cewa Turkawa, Larabawa da Kurdawa zasu iya kaiwa junansu farmaki?

Ko me ya sa Amurka ke yin haɗaka da taimakawa kungiyoyin ta'addanci?

Shin menene dalilan da suke sanya Amurka yin hakan?

Dalili lsra'ila

A duk lokacin da Amurka ke jawabi akan wadannan lamurkan da  take yi tana bayyana cewar tana yi ne domin ƙalubalantar DEASH da lran, amma wannan ba dalilai bane da hankali zai iya ɗauka.

Idan muka dubi matakan Amurka marasa inganci da gaskiya zamu ga cewa dukkanin salonta sun ta’alaƙa ne akan inganta lamurkan cin zarafin da ke yi lsra'ila a yankin. Matakan Amurka a yankin sun saɓawa ƙa'idojinta; sunka kuma marawa ra'ayin lsra'ila baya. Ko shakka babu wannan matakan na Amurka domin inganta lsra'ila suna tattare da nauyi da kuma ƙalubale akan Amurka, lsra'ila da ma Yahudawa da basa da ra'ayin yahudanci.

Nauyin lsra'ila akan Amurka:

Amurka ta ajiye ra'ayinta gefe guda: A zamanin yau kowa yasan cewa dangantakar ƙasashe na gudana ne akan ra'ayin dake tsakanin kasashen. Game da lsra'ila Amurka ta yi jifa da ra'ayinta da buƙatunta cikin kwandon shara.

Goyawa lsra'ila baya akan cin zarafi  da mamayar ƙasar Falasdinu da take yi sun saɓawa ɗabi'un adalci, kare hakkin dan adam da zaman lafiya, sun kasance lamurkan dake kara zubar da darajar Amurkan a fadin duniya.

Ƙalubalantar al'ummar yankin da ƙasashen yankin: Ɗaukar matakan da zasu kare ra'ayin lsra'ila kachal a yankin da kuma yin kalaman da zasu kasance ƙalubale ga al'ummar yankin zasu sanya mutanen yankin su dauki kwararan matakai koda gwamnatocin yankin basu ce uffan ba.

Haƙiƙa kasancewar yadda Amurka ta mayarda da matakanta na lsra'ila ya sanya gurguntar matakan nata

Shirin ƙara mayarda lsra'ila azzalumar ƙasa:

Yadda Amurka ke ci gaba da tallafawa lsra'ila duk da ire-iren ayyukan kin ƙari munana da take ayyanar wa a Gabas ta Tsakiya, shiri ne dake da niyyar ƙara mata ƙarfin gwiwar ci gaba da kai hare-hare da cin zalin da take yi a yankin.

Haɓakar ƙyamar Yahudawa: ldan dai aka ci gaba da tallafawa lsra'ila domin ci gaba da cin zarafin da take aiyanarwa, da kuma daukar matakan da sunka saɓawa hakkin dan adam ko shakka babu kyamar yahudawa zai ƙaru a fadin duniya. Ya dai kamata mu san cewa nuna wariyar launin fata da kyamar ko wacce irin al'umma wannan ba abu ne da za'a yarda da shi ba.

Ƙaruwar matsalolin tsaro  ga lsra'ila: A haƙiƙanin gaskiya wannan tallafawa da Amurka ke baiwa lsra'ila domin ci gaba da cin zarafi a yankin bawai inganta tsaronta yake yi ba gurbata su yake , ba kuma karfafata yake yi ba; yana ƙara gurgunta tane  a yankin dama duniya baki ɗaya.

Shin ko me ya sanya Amurka ci gaba da tallafawa lsra'ila akan wadannan cin zarafin da take yi, duk da cewa hakan ya jawo wa Amurka bakin jini cikin kankanin lokaci dama matsaloli a cikin dogon zango. Kai har ma ita lsra'ila tana fuskantar matsalolin na tsawon lokaci akan wannan gurguwar matakin da Amurka ke tallafa mata akai. Amsar wannan tambayar zai kasance maudu'i mai zaman kansa wanda zamu yi sharhi akai anan gaba. Anan ya kamata mu fahimci cewa, duk da irin baran da faɗi-tashin da lsra'ila ke yi, a ƙasar Amurka ba kowa ne ke goyon bayan muhimmiyar ƙasa ƙamar Amurka ta rinƙa goyowa ƴar kucucin ƙasa domin cin zarafin al'ummar yankinta ba.Labarai masu alaka