Iran ta daure wani tsohon sojan ruwan Amurka

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Behram Kasimi ya gasgata labarin gurfanar da wani tsohon sojan ruwan Amurka Michael White da aka yi a garin Mashhad tare da aika shi zuwa gidan maza.

Sanarwar da Kasimi ya buga a shafin yanar gizon M’aikatar ta ce, a baya an yi shari’ar White a garin Mashhad na jihar Horasan kuma sun sanar da ofishin Kare Manufofin Amurka dake birnin Tehran.

Kasimi ya karyata cewar wai ana zaluntar White a gidan kurkukun da aka kai shi.

Jaridar New York Times ta Amurka ta ce, tun wana Yulin 2018 ake tsare da Michael White a kasar Iran.

Jaridar ta bayyana cewar bayan tuntubar iyalan White dan asalin jihar California, sun shaida ya tafi Iran wajen budurwarsa wanda kuma a karshe aka kama shi tare da daurewa.Labarai masu alaka