Pompeo: Tabbas dakarun Amurka za su fita daga Siriya

Ministan Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya bayana cewa, da gaske Shugaba Trump yake kan batun janyewar sojojinsu daga Siriya, kuma sun fahimci irin barazanar da ‘yan ta’adda ke wa Turkiyya a saboda haka za su taimaki Turkiyyan.

Rubutacciyar sanarwar da Ma’aikatar harkokin Wajen ta Amurka ta fitar ta ce, Pompeo da yake ziyartar wasu kasashen Gabas ta Tsakiya ya zanta da manema labarai a ofishin jakadancin Amurka dake Irbil inda ya ce “A bayyane yake karara Trump na son janyewa daga Siriya.”

Da wani dan jarida ya tambaye shikan barazanar da ‘yan ta’addar aware na PKK/YPG suke wa Turkiyya kuma yaya alakarsu za ta kasance, sai ya ce suna tattaunawa da dukkan bangarorin biyu.

Ya ci gaba da cewa “A yanzu muna ta tattauna yada sojojinmu za su fita daga Siriya slaim alim. Amma kafi su fice muna so mu tabbatar mun gama yakar ‘yan ta’addar Daesh baki daya.”

Da wani dan jarida ya tambaye shi game da kalaman Shugaba Recep Tayyip Erdogan kan cewar ‘yan ta’addar PKK/YPG na wa Turkiyya barazana sai ya ce “Erdogan ya bayyana ‘yan ta’adda na musu barazana a rayuwarsu. Kuma mu ma mun fahimci irin barazanar da ‘Yan ta’addar suke wa Turkiyya. A kan wannan batu za mu ba wa Turkiyya goyon baya. A shirye muke mu marawa dukkan kasashen da suke yaki da masu tsaurin ra’ayi ko ‘yan ta’adda. Wannan ya hada da Turkiyya da sauran kasashe.”Labarai masu alaka