Trump ya kori ministan shari'a

Ministan harkokin shari'ar ƙasar Amurka Jeff Session ya yi murabus daga mukaminsa sanadiyar matsin lambar da ya fuskanta daga fadar gwamnati akan hakan.

Trump ya kori ministan shari'a

Ministan harkokin shari'ar ƙasar Amurka Jeff Session ya yi murabus daga mukaminsa sanadiyar matsin lambar da ya fuskanta daga fadar gwamnati akan hakan.

Session ya bayyana cewar ya ajiye muƙaminsa ne domin shugaba Donald Trump ya nemi hakan.

A wasiƙar murabus dinsa Jeff Session ya yi jawabi kamar haka: "Ya shugaban ƙasa, ina mai miƙa takardar ajiye muƙami na a matsayin ministan Shari'a kamar yadda ka nema, ina mai gode maka akan damar da ka bani"

Session ya kuma godewa dukkanin ma'aikatan ma'iakatar shari'ar ƙasar akan haddin kai da suka bashi lokacin mulkinsa.

A ɗayan barayin kuma, shugaba Donald Trump ya yaɗa a shafinsa ta Twitter inda ya godewa Jeff Session akan irin aikin da ya gudanar, ya kuma yi masa fatan alheri a rayuwarsa, Trump ya bayyana cewar za'a bayyana wanda zai maye gurbinsa na zuwa gaba.

A halin yanzu dai an bayyana sakataren ma'aikatar shari'ar Matthew G. Whitaker a matsayin wanda zai maye gurbin Session na wuccin gadi.

 Labarai masu alaka