"Ba zanci gaba da kasancewa minista a gwamnatin da bata bin ka'ida ba"

Ministan sufuri da lamurkan biranen kasar Iran Abbas Ahundi ya ajiye mukaminsa sakamakon rashin fahimtar dake farauwa tsakaninsa da gwamnati akan lamurkan bunkasar birane da tattalin arzikin kasar.

Ahundi, ya yada a shafukansa na sadar da zumunta da cewar ya mikawa shugaba Hasan Ruhani takardar murabus dinsa tun a 1 ga watan Satumba.

Abbas Ahundi, ya kara da cewa bai samu damar gudanar da aiyuka da zasu kawo canji mai inganci a biranen kasar ba, kuma yadda hukuma ke katsalandar a cikin harkokin tattalin arziki da kuma rashin fahimtar juna da ke afkuwa bai kamata in ci gaba da zama a matsayin minista ba.

Ya kara da cewa bai kamata a yi katsalandar ga harkokin doka da tattalin arzikin kasa ba. Ahundi ya tabbatar da cewa tun bayan da Amurka ta sanya wa kasar takunkumi ake ta daukar matakan dake sabawa kai'dojin doka da tattalin arziki.

Ahundi wanda a baya ya ajiye mukaminsa har sau uku amma Ruhani bai amince da murabus dinsa ba ya fito karar  ya shaida masa da cewa "Ka iya neman wanda yafi dacewa da kai a maimako na"

Shugaban hurdar jama'a a ma'aikatan Kasim Biniyaz ya bayyanawa gidan talabijin kasar murabus din minista Ahundi.

Shugaba Hasan Ruhani dai ya tube ministan ayyuka Ali Rebii a ranar 8 ga watan Agusta da kuma ministan kudi Mesud Kerbasiyan a ranar 26 ga watan Agusta bayan majalisar sun kalubalancesu akan rashin iya aiki.

 Labarai masu alaka