Sojin Yaman da 'yan tawayen Houthi sun fafata kazamin rikici a Yaman

Mutane 28 aka kashe sakamakon kazamin rikicin da sojojin Yaman suka fafata da 'yan tawayen Houthi a garin Bayda.

Sojin Yaman da 'yan tawayen Houthi sun fafata kazamin rikici a Yaman

Mutane 28 aka kashe sakamakon kazamin rikicin da sojojin Yaman suka fafata da 'yan tawayen Houthi a garin Bayda.

Majiyoyin kasar sun ce, 'yan tawayen na Houthi ne suka kai hari a tsaunin Zahr da ke hannun sojin gwamnati. 

Sakamakon mayar da martani da sojin suka yi ne ya zanyo fafata rikici tsakanin bangarorin 2.

An kashe sojoji 10 da 'yan tawaye 18 a arangamar. 

An bayyana cewar an samu jikkata daga kowanne bangare.

Tag: Bayda , Houthi , Yaman

Labarai masu alaka